Home General Za mu biya kudaden daliban Kano da Ganduje ya gaza biya a...

Za mu biya kudaden daliban Kano da Ganduje ya gaza biya a Cyprus – Gwamna Abba

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya dauki matakin magance matsalolin da daliban Kano wadanda gwamnatin Ganduje ta tura karatu kuma suka kasa karbar shaidar kammala karatunsu.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa PRNigeria a ranar Litinin, ta bayyana cewa gwamna Yusuf ya yi wata muhimmiyar ganawa da mahukuntan jami’ar Near East da ke Cyprus domin shawo kan lamarin.

Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan batun bayar da satifiket ga daliban Kano da suka kammala karatunsu a shekarar 2015 zuwa 2019.

Da yawa daga cikin wadannan daliban da aka yaye, musamman wadanda suka yi karatu a fannonin aikin likitanci da aikin jinya, sun kasa samun damar yin aikin da suka koya, sakamakon gaza biyan kudin makaranta da gwamnatin Ganduje ta yi.

Gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin babban koma-baya, ba wai ga daliban da abin ya shafa ba, har ma da jihar, wadda take da bukatar kwararru jami’an kula da lafiya.

Gwamnana Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa zata biya duk kudaden da ake bin daliban domin su karɓi Satifiket dinsu don su fara amfani da abun da suka koya domin amfanin al’umma.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp