Ministan harkokin Jiragen Sama da kula Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ya bayyana cewa Hukumar Tsaro ta DSS ba ta da hurumin bincikar jakunkuna a filayen jiragen saman Najeriya.
ya bayyana hakan ne ta cikin shirin The Morning Show na Arise News TV a ranar Lahadi, Keyamo ya yi bayani kan sabbin matakai da aka dauka don rage tsangwama ga fasinjoji da kuma saukaka tsaro a filayen jiragen sama.
ya kuma ambaci wannan dabi’ar a matsayin wata ta’ada da ba ta da amfani kuma ba ta cikin aikace-aikacen da hukumar ke da alhakin su kai tsaye.
Ya jaddada cewa DSS ya kamata ta mayar da hankali kan bincikar mutanen da za su iya zama barazana ga tsaro, musamman ma waɗanda ke tafiya zuwa ƙasashen waje, maimakon gudanar da binciken kayan jakunkuna, wanda ba ya cikin manyan ayyukanta.
“DSS, ba ku da hurumin bincikar jakunkunan mutane. Ku mayar da hankali kan bincikar mutane da ke fita daga ƙasar,” in ji Keyamo.