Home General Tinubu na son ganin babu wanda ya kwana da yunwa a Najeriya...

Tinubu na son ganin babu wanda ya kwana da yunwa a Najeriya – Minista

Shugaban kasar Bola Tinubu, ya ce samar da abinci shi ne babban abin da gwamnatinsa tafi ba wa muhimmanci.

Karamin ministan noma na kasar, Aliyu Abdullahi, ne ya bayyana hakan inda yace tun bayan da aka rantsar da shugaba Tinubu a watan Mayun 2023, gwamnatinsa ta bullo da shirye-shirye da dama domin tabbatar da an wadata kasar da abinci.

Cikin wata hira da gidan talbijin na Sunrise Daily ya yi da ministan, ya ce a cikin shirye-shirye Tinubu, samar da abinci shi ne kan gaba haka kuma bunkasa aikin noma ma na cikin manyan muradun shugaban kasar saboda baya ga samar da abinci da bangaren noma zai yi zai kuma bunkasa tattalin arzikin kasa.

Aliyu Abdullahi, ya ce shugaba Tinubu, ya damu matuka da matsalar karancin abincin da ake fama da ita a kasa,inda ya ce a wasu lokutan shugaba Tinubun kan sanar da su cewa babban burinsa shi ne ya kai al’ummar Najeriya matsayin da babu wanda zai kwana da yunwa.

Hauhawar farashin kayan abinci da ake fama da ita a Najeriya a baya bayannan, ta jefa miliyoyin mutane cikin yunwa a Najeriya.

A wannan yanayi da ake ciki, gwamnatin tarayyar Najeriya ta bullo da wasu hanyoyi na saukaka rayuwa ciki har da rabon tallafin abinci ga miliyoyin ‘yan Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp