Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa Nwakuche Ndidi, a matsayin shugaban riƙo na hukumar kula da gidajen yarin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar hukumar tsaro ta sibil difens da hukumar kashe gobara da ta shige da fice, Ja’afaru Ahmed ya ce naɗin Ndidi zai fara aiki daga ranar 15 ga watan Disamba.
Naɗin nasa na zuwa ne bayan ƙarewar wa’adin shugaban hukumar na yanzu, Haliru Nababa.
A ranar 18 ga watan Fabrairu ne dai tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya naɗa Nababa a muƙamin.
An haifi Nwakuche Ndidi ranar 26 ga watan Nuwamban shekarar 1966 a garin Oguta na jihar Imo.
Kafin naɗinsa kan muƙamin shi ne mataimakin shugaban hukumar mai lura da horaswa.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1487 days 8 hours 50 minutes 3 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1469 days 10 hours 31 minutes 28 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com