Sabuwar ƙungiyar matasan arewacin Najeriya ta LND ƙarkashin jagorancin shugabanta kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ta nemi a yi gyaran fuska ga sabon ƙudirin haraji mai cike da cece-kuce da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya gabatarwa majalisar dokokin kasar.
Read Also:
Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja a wajen gabatar da rahoton kwamitin kwararru da ta kafa domin yin nazari kan kudirin sake fasalin harajin da ya janyo cece-kuce a ƙasar.
Tun bayan gabatar da ƙudirin da shugaba Tinubu ya yi, na sake fasalin dokar haraji, ya haifar da zazzafar muhawara a fadin ƙasar, masamman masu fada a ji a yankin arewacin ƙasar da ke zargin zai haifar da koma baya ga yankin.