Cibiyar rajin kyautata ayyukan majalisar dokoki da yaƙi da rashawa a Najeriyar wato CISLAC, ta yi kira da a guji yin cushe a kasafin kuɗin 2025, tare da kira ga gwamnatin tarayya ta tabbatar da kasafta kuɗaɗe kan abubuwan da ƴan ƙasar ke buƙata.
A wata sanarwa da shugaban cibiyar, Auwal Ibrahim Musa (Rafsanjani), ya fitar, CISLAC ta ce cushe a kasafin kuɗi da kasafta kuɗaɗe masu yawa a ayyukan da ba su cancanta ba, bai dace ba, inda ya yi misali da kasafta wa ma’aikatar wasanni da ta Neja Delta kuɗaɗe waɗanda an riga an rufe su.
Da take amfani da rahoton babban mai binciken kuɗi na bana, CISLAC ta bayyana wasu kuɗaɗe da aka cire da suka sha banbam, inda ta ce an cire sama da naira biliyan 197.72 domin wasu ayyuka a ma’aikatu tsakanin 2020 da 2021 ba bisa ƙa’ida ba.
Cibiyar sai ta yi kira ga majalisar da ta yi nazarin kasafin kuɗin cikin mutunci da nagarta.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1486 days 20 hours 2 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1468 days 21 hours 41 minutes 27 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com