Home General PDP ta dora alhakin talaucin da ‘ya Nijeriya suke ciki kan APC

PDP ta dora alhakin talaucin da ‘ya Nijeriya suke ciki kan APC

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta ce turmutsutsun da aka samu a Najeriya guda uku cikin ƙanƙanin lokaci ya nuna cewa akwai talauci da yunwa a ƙasar, wanda a cewarta yana da nasaba da irin mulkin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.

Kakakin PDP na ƙasa, Debo Ologunagba ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da tashar Channels ta ruwaito, inda ya ce turmutsutsun da ake samu wajen rabon abinci abu ne da za a iya kiyaye aukuwarsu.

“PDP na baƙin ciki yadda gwamnatin APC te ɗaiɗaita tattalin arzikin ƙasar nan tare da jefa miliyoyin mutane cikin ƙangin talauci da yunwa, inda mutane da dama ba sa iya cin abinci, har wasu suke gwammace tafiya ƙasashen waje suna aiki masu wahala.

“Akwai takaici ganin duk da ɗimbin arzikin da Najeriya ke da shi, ƴan ƙasar suna rayuwa cikin ƙunci, har ta kai suna mutuwa wajen karɓar abinci.

PDP ta kuma yi kira ga gwamnatin ta sake duba matakan da ta ɗauka da suka jawo tsadar rayuwa a ƙasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp