Home General Hukumar Custom a Najeriya ta rushe rundunarta dake da sintiri a iyakokin...

Hukumar Custom a Najeriya ta rushe rundunarta dake da sintiri a iyakokin ƙasar

Hukumar hana fasa ƙwauri ta Najeriya Custom ta rushe rundunarta ta musamman dake gudanar da sintiri a kan iyakokin ƙasar yayin da ake tsaka da zarginsu da cin zarafin jama’a.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar a Najeriya Abdullahi Maiwada a wata sanarwa da ya fitar ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan samun amincewar haka daga ofishin mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan sha’anin tsaro.

Majalisar wakilan Najeriya a ranar 11 ga watan disamba ta ɗorawa kwamitinta mai lura da hukumar kwastam ya binciki ayyukan da hukumar ke yi a iyakokin ƙasar bayan zarginsu da aka yi da taimakawa ƴan sumoga da kuma cin zarafin ƴan Najeriya.

Wannan ya biyo bayan wani ƙudirin gaggawa da ɗan majalisa Sesi Whingan ya gabatar, inda ya ce maimakon daƙile simoga jami’an kwastam a iyakokin ƙasar na bigewa da taimakawa masu fasa ƙwauri.

To sai dai mai magana da yawun hukumar hana fasa ƙwaurin ta Najeriya a sanarwar da ya fitar ya ce matakin rushe tawagar na a matsayin wani yunƙurin ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro wurin ƙarfafa tsaro a iyakokin ƙasar.

Maiwada ya ce rushe wannan tawaga ba zai kawo tsaiko ba ko kaɗan dangane da tsaron iyakokin Najeriya ko kuma kasuwanci, illa hakan wani mataki ne da zai zamanantar da ayyyukan hukumar ta Custom da ayyukanta da kuma tabbatar da tsaron Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp