Home General Rundunar sojin Najeriya ta ƙaryata kai harin kuskure kan fararen hula a...

Rundunar sojin Najeriya ta ƙaryata kai harin kuskure kan fararen hula a Sokoto

Rundunar sojojin haɗin gwiwa ta Najeriya ta Operation Fansan Yamma, ta buƙuci jama’a su rinƙa dogara da ingantattun bayanai don hana yaɗa rahotannin ƙarya da ke haifar da shakku game da ayyukanta.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, wacce ke mai da martani game da rahotannin da ke cewar wani jirgin yaƙin sojin Najeriya ya kai harin bam wasu kauyuka a ƙaramar hukumar Silame da ke jihar Sakoto, inda ake fargabar mutane da dama sun rasa ransu.

Rundunar ta ce sai da ta tabbatar da cewar inda ta kai harin a garuwan Gidan Sama da kuma Rumtuwa, suna da alaƙa da ƙungiyar ƴan ta’adda ta Lakurawa.

Laftanar Kanar Abdullahi ya ce rundunar na gudanar da dukkan ayyukanta ne bayan tattara bayanan siri da kuma bincike.

Wasu majiyoyi sun ruwaito cewa mutane 10 ne suka rasu yayin hare-haren, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Shugaban Ƙaramar Hukumar ta Silame, Alhaji Abubakar Muhammad Daftarana, ya tabbatar da faruwar harin, sai dai ya ce har yanzu suna aikin tantance irin ɓarnar da harin ya yi.

Tuni dai gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya ziyarci kauyukan da abin ya faru don jajantawa iyalan waɗanda ibtila’in ya shafa, tare da yin alkawarin kafa kwamiti don gudanar da bincike akai.

Na kaɗu matuka da faruwan wannan lamarin, ba da gangan jami’an tsaro suka yi ba, haƙiƙa sun je kai wa ƴan ta’addan hari ne, sun yi nasarar kashe ƴan ta’adda a hari na farko da na biyu, sai dai an samu kuskure a na uku.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da ake samun hare-heren kuskure kan fararen hula a Najeriya, wanda kuma ke haifar da asarar dimbin rayukan al’umma.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp