Home General Sokoto: Babu hujjar kashe mutanen da babu ruwansu – Atiku

Sokoto: Babu hujjar kashe mutanen da babu ruwansu – Atiku

Tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya ce babu wata hujjar da za a bayar kan kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Atiku ya bayyana haka a saƙonsa na jaje game da ibtila’in da ya auku a jihar Sokoto, inda hare-haren sojoji ‘bisa kuskure’ ya yi ajalin aƙalla mutum 10, ya jikkata wasu.

Atiku ya ce yadda kuskuren ke maimiatuwa ya sa ake tambayar wane darasi aka ɗauka a baya.

A cewarsa, “A ranar 3 ga Disamban 2023, gomman mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba ne suka rasu a Tudun Biri da ke Kaduna. Shin mutum nawa za su ƙara mutuwa kafin a ɗauki mataki? Duk da cewa yana da kyau a ƙaddamar da hare-hare kan ƴanbindiga, amma ai akwai buƙatar a yi amfani da ƙwarewa.”

“Babu wata hujjar da za a bayar kan kashe mutanen da babu ruwansu. Irin haka na nuna rashin ƙwarewa da tauye haƙƙin ɗan’adam.”

Ya ce hakan zai sa mutane su kasa bambance masu kare su da waɗanda suka kashe, inda ya ce dole a kawo ƙarshen irin wannan kashe-kashen bisa kuskure.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp