Harin ISWAP ya hallaka sojojin Najeriya shida a jihar Borno

Rahotannin daga jihar Borno dake Arewa maso gabashin Nijeriya na bayyana cewa Mayaƙa masu alaƙa da ƙungiyar ISWAP sun hallaka sojojin kasar shida yayin wani hari da suka kai kan sansaninsu, kamar yadda kamfanin yada labarai na AFP ya ruwaito

AFP ya ambato jami’an sojin Najeriya biyu na cewa maharan na ƙungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP) sun far wa sansanin da ke Sabon Gari a ƙaramar hukumar Damboa ranar Lahadi da tsakar dare.

Rahotonni sun ce sun cinna wa sansanin wuta tare da ababen hawan da ke cikinsa.

“An kashe mana sojoji shida a harin na Iswap da suka kai sansanin bayan zazzafar musayar wuta,” kamar yadda ɗaya daga cikin jami’an ya faɗa wa AFP.

Ɗaya jami’in ya ce jirgin sojin sama da aka aika daga binrin Maiduguri, mai nisan kilomita 100, shi ne ya kori maharan.

“Hare-hare ta sama ya kashe ‘yanbindigar da yawa, ya lalata motoci da makamansu,” in ji majiyar ba tare da bayar da yawan adadi ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com