Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya tura sabbin Kwamishinoni 7n da ya rantsar zuwa ma’aikatun da zasu kula masa dasu.
Kwamishinan shari’a na jihar kuma babban lauyan Gwamnati, Barista Haruna Isa Dederi ne ya rantsar da sabbin kwamishinonin 7, da sabbin manyan sakatarorin gwamnati guda 6 da aka daga likkafarsu, dama sauran masu baiwa gwamna shawara guda 13.
Sabbin Kwamishinonin dama ma’aikatun da aka tura su sune;
1. Alhaji Shehu Wada Sagagi – Ma’aikatar kasuwanci da zuba jari
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
2. Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya – Ma’aikatar yada Labarai
3. Dakta Dahir Muhammad Hashim – Ma’aikatar Muhalli
4. Abdulkadir Abdussalam -Ma’aikatar Raya Karkara
5. Dakta Isma’ila Aliyu Dan Maraya – Ma’aikatar Kudi
6. Dakta Gaddafi Sani Yakubu – Ma’aikatar Makamashi
7. Dakta Nura Iro Ma’aji – Ma’aikatar kula da kwangiloli da bibiyar ayyukan gwamnati
A karshe Gwamnan ya taya su murna tare da bukatar su rike gaskiya da amana, domin kiyaye rantsuwar da suka yi na yiwa jama’a aiki.











