Najeriya da China sun amince su ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin makamashi, da tsaro, da harkokin kuɗi, kamar yadda ministocin harkokin wajen ƙasashen sukam bayyana yau Alhamis.
Ministan Harkokin Wajen China Wang Yi na ziyara a Najeriya ne a matsayin wani ɓangare na ziyarar aiki a ƙasashen Afirka huɗu domin faɗaɗa tasirin ƙasarsa a nahiyar.
Mista Wang ya ce China za ta duba buƙatar da Najeriya ta gabatar mata ta faɗaɗa yarjejniyar amfani da takardun kuɗin ƙasar na Yan.
A ɓangaren tsaro kuma, Wang ya ce China za ta dinga goya wa Afirka baya kodayaushe a zauren tsaron tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.
“Za mu yi aiki da Afirka wajen inganta tsaro da kuma cim ma zaman lafiya ta hanyar ayyukan more rayuwa,” in ji shi.