Gwamnatin Najeriya ta buɗe kwalejin horas da matasa kan ƙirƙirarriyar basira a kyauta

Gwamnatin Najeriya ta ce ta ƙaddamar da wani shiri na horar da matasa game da sanin makamar ƙirƙirarriyar basira wato Artificial Intelligence (AI) ta intanet.

Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha Uche Geoffrey Nnaji ya ce shirin wanda aka ƙaddamar ranar Talata, an yi masa suna AI Academy – wato kwalejin ƙirƙirarriyar basira.

Najeriya ta ƙaddamar da shirin bisa haɗin gwiwa da ƙungiyar ƙasashe rainon Ingila ta Commonwealth.

“AI Academy za ta horar da ɗalibai, da matasa, da ma’aikatan gwamnati wajen shawo kan matsaloli da kuma ƙirƙirar damarmaki ta hanyar amfani da ƙirƙirarriyar basira,” in ji ministan.

Ya ƙara da cewa za a rufe yin rajista a shafin kwalejin ranar 30 ga watan Janairun nan.

Ministan ya ce masu sha’awa na iya a ziyartar wannan adireshin an domin yin rajista.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com