Home General Gwamna Yusuf ya biya biliyan 16 ga yan fansho a Kano

Gwamna Yusuf ya biya biliyan 16 ga yan fansho a Kano

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na cigaba da biyan yan fansho hakkokinsu domin inganta jin dadi da walwalarsu.

” Gwamnatinmu ta damu da walwalarku shi yasa tun da na zo nake cigaba da biyan wadanda suka kammala aiki hakkokinsu, wanda a yau na kaddamar da kashi na uku na biyanku kudaden gama Aiki wato Gratuity”.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa PRNigeria.

Ya ce daga daga hawan gwamnan Yusuf Kan karagar mulki ya biya kimanin naira Biliyan 16 ga yan fansho wanda ya ce hakan zai kara inganta jin dadi da walwalarsu da ma cigaban tattalin arzikin jihar Kano.

” Karon farko na ware biliyan 6 domin biyan wadanda suka gama aiki daga matakin albashi na 10 zuwa kasa, yayin da a kashi na biyu muka biya biliyan 5 ga wadanda suka kammala aiki sakamakon cika shekaru 35″. Inji Abba Kabir

Sanarwar ta kara da cewa gwamna Yusuf ya yi alkawarin cigaba da biyan yan fansho hakkokinsu, inda yace bai dace a bar su haka ba, idan aka yi la’akari da irin gudunmawar da suka bayar don cigaban jihar Kano a lokacin da suke aiki.

Ya ce zai cigaba da biyan yan fansho hakkokinsu ba tare da bata lokaci ba, inda ya ba su tabbacin za kuma a cigaba da biyansu kudinsu na wata-wata ba tare da wata matsala ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp