Majalisar dokokin Najeriya ta bayyana damuwa game da babban rashin daidaito tsakanin kudaden da akan kashe wajen ayyukan raya kasa da wadanda akan kashe don gudanar da ayyukan ma’aikatu na yau da kullum a kasafin kudin bara.
‘Yan majalisar sun yi nuni da yadda aka yi kwauron sakin kudi don aiwatar da manyan ayyukan raya kasa ga ma’aikatu da sassa da hukumomin gwamnati.
‘Yan majalisar dokokin sun ce abin da aka samu bai taka kara ya karya ba, kuma ba zai kai a ce an gudanar da ayyukan yadda ya dace ba a kasafin kudin na bara.
Daya daga cikin ‘yan majalisar Injiniya Satomi Ahmed, ya shaida wa BBC cewa an yi shirin aiwatar da karashen kasafin kudin na bara har zuwa watan Yunin bana, ta yadda za a rika aiwatar da shi tare da na wannan shekara.
Yace : “Babbar damuwar ita ce rashin fitar da kudaden da ya kamata a yi manyan ayyuka na ci gaban kasa, rashin hakan shi ne ya haifar da halin da Najeriya ke ciki, da rashin ci gaban gwamnati da matsalolin da ta ke fuskanta.
Ba a bai wa ma’aikatu daban-daban kudaden aiwatar da ayyuka na musamman, kamar fannin noma da ta ttalin arziki, da ma’aikatar raya yankin Arewa maso yammacin Najeriya ba.
Wasu ma’aikatun sun samu kashi 40, wasu kuma kashi 30 cikin 100, kai akwai wasu ma da ba su samu kashi 20 ba a kasafin kudin shekarar 2024,” in ji Satomi.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1488 days 8 hours 17 minutes 6 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1470 days 9 hours 58 minutes 31 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com