Home General Kotun daukaka kara a Abuja ta yanke hukunci kan dambarwar Masarautar Kano

Kotun daukaka kara a Abuja ta yanke hukunci kan dambarwar Masarautar Kano

Kotun daukaka kara dake zaman ta a Abuja ta yanke hukuncin cewa babbar kotun tarayya ba ta da hurumin saurarar duk wata kara da ta shafi dokar masarautu.

Haka zalika kotun ta ce sashi na 251 na kundin tsarin mulkin Nijeriya ya yayi bayani dalla-dalla kan harancin kotun tarayya ta shiga al’amarin da ya shafi masarautu.

Kotun tace tsohon sarkin na kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya gaza gabatar da hujjojin da za su gasgata da’awarsa na cewa an tauye masa hakkinsa matsayin sa na dan Adam.

Idan za a iya tunawa Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero bayan da gwamnatin Kano ta ayyana cire shi, ya garzaya gaban babbar kotun tarayya dake Kano domin kalubalantar matakin gwamnatin.

Aminu Ado Bayero yana da’awar cewa an take masa hakkinsa a matsayinsa na dan adam, don haka yake neman kotun da duba labarin, sai dai gwamnatin Kano ta ce kotun tarayyar bata da hurumin saurarar kara lamarin da yasa ta tafi kotun daukaka kara domin nemo fassara.

Kotun daukaka Karar ta ce Babbar kotun tarayyar ba ta da hurumin kamar yadda kotun koli ta Kasa ta taba yanke hukuncin akan shari’ar Tukur da gwamnan gongola.

Kotun ta ce kotun da ke da hurumin shari’ar masarautu a tsarin mulkin Nijeriya, ita ce babbar kotun jiha ba babbar kotun tarayya ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp