Home General INEC ta buƙaci naira biliyan 126 a kasafin kuɗinta na 2025

INEC ta buƙaci naira biliyan 126 a kasafin kuɗinta na 2025

Hukumar zaɓen Najeriya ta yi buƙaci a ware mata naira biliyan 126 a matsayin kuɗin da za ta kashe a shekarar 2025.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka ranar Juma’a, a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin haɗin gwiwa na majalisar dokokin ƙasar don kare kasafin kuɗin hukumar na 2024.

Tun da farko shugaban hukumar ya yi watsi da naira biliyan 40 da aka ware wa hukumarsa a kasafin kuɗin wannan shekara.

Yana mai danganta hakan da ƙaruwar tsadar abubuwa a Najeriya ciki har da kayayyakin aikin zaɓe.

”Zaɓe a Najeriya ya kasance wani babban abu da ke buƙatar wadatattun kuɗi, don haka abin da muke buƙata a wannan shekara ya kai naira biliyan 126, kuma muna da takardun da ke ɗauke da cikakkun bayanan yadda za mu kashe waɗannan kuɗaɗe da muka buƙata”, in ji Farfesa Yakubu.

Daga cikin ayyukan da ya ce hukumar za ta gudanar a shekarar sun haɗa da cigaba da aikin rajistar masu zaɓe, da shirya zaɓukan wasu jihohin a bana, da sauya wasu kayyakin zaɓen da suka lalace da gyara ofisoshin hukumar da ke wasu ƙanann hukumomi.

Haka kuma ya ce shekarar 2025, shekara ce mai muhimmanci ga hukumar wajen shirya zaɓukan 2027.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp