Home General Rikicin masarautar Kano: Mun gamsu da hukuncin kotun daukaka kara ta yanke...

Rikicin masarautar Kano: Mun gamsu da hukuncin kotun daukaka kara ta yanke – Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano, ta nuna Jin dadinta da hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke dangane da batun da ya shafi Masarautar Kano na dawo Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu.

Kwamishinan shari’a na Jihar Kano Barrister Haruna Isah Dediri ya bayyana gamsuwarsa Lokacin da ya ke ganawa da manema labaru.

Dederi ya ce Hukuncin da kotun daukaka karar ta yi, ya soke hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a baya, ya kuma tabbatar da matakin da gwamnatin Kano ta dauka dangane da nade-nade, mukamai da Kuma gyare-gyare a masarautar Kano.

”Duk wasu hukunce-hukunce da babbar kotun tarayya ta yi a baya wadanda suka shafi rikicin masarautu a Kano ya zama rusashshe, idan kai la’akari da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a jiya”. Inji Barr. Dederi

Dederi ya ce a madadin gwamnatin jihar Kano suna yabawa bangaren shari’a na kasar nan saboda yadda ya yanke hukuncin ba tare da daukar wani bangare ba, dangane da rikicin masarautu a Kano.

“Da wannan hukuncin za gwamnatin jihar Kano za ta tabbatar da cigaba da aiki kafa da kada da masarautun gargajiya domin ciyar da jihar Kano gaba ta kowacce fuska”. A cewar Kwamishinan shari’a

Daderi ya yi kira da hukumomi da ma’aikatun gwamnati da kamfanoni da Kungiyoyi da daidaikun al’umma da su tabbatar da bin umarnin da kotun daukaka kara ta yi na tabbatar da abun da gwamnatin Kano ta yi akan abun da ya shafi Masarautar Kano.

Ya ce gwamnatin Kano tana kira ga dukkanin bangarorin da abun ya shafa da su Ajiye komai su zo a hada hannu da su don cigaban jihar Kano.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp