Hajjin 2025: Gwamnatin Najeriya ta zaɓi kamfanonin jirage huɗu domin jigilar maniyyata

Gwamnatin Najeriya ta amince da kamfanonin jiragen sama guda huɗu domin jigilar maniyyata Hajjin bana.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban hukumar jin daɗin alhazai ta Najeriya, NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman ya fitar a ranar Lahadi, inda ya ce an zaɓi kamfanoni huɗu ne daga cikin guda 11 da suka nuna sha’awar aikin jigilar maniyyatan, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

Ya ce kamfanonin huɗu su ne: Air Peace Ltd, da wani kamfanin ƙasar Saudiya mai suna Fly-Nas da Max Air da kuma UMZA Aviation Services Ltd.

Ya ƙara da cewa kwamiti mai mutum 32 da aka kafa a ranar 26 ga Nuwamban bara ne suka zauna suka tantance kamfanonin, kafin suka amince da guda huɗun

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1486 days 2 hours 49 minutes 20 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1468 days 4 hours 30 minutes 45 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com