Home General Jam’iyyar LP a Nijeriya ta zargi Tinubu kan batan wasu kudi a...

Jam’iyyar LP a Nijeriya ta zargi Tinubu kan batan wasu kudi a hukumar kidaya

Jam’iyyar adawa ta Labour a Najeriya ta zargi gwamnatin kasar da gazawa wajen yi wa ‘yan Najeriya bayani kan yadda aka yi da naira biliyan 234 wani bangare na kudin kidayar jama’a da aka shirya gudanarwa a shekara ta 2023, da aka dakatar.

Jam’iyyar na zargin cewa an karkatar da kudaden ne wajen yakin neman zaben 2023.

Jam’iyyar ta Labour ta ce a karkashin gwamnatin da ta gabata ta shugaba Muhammadu Buhari, hukumar kidayar jama’a ta kasar ta bukaci a sahale mata kashe naira biliyan 800 domin gudanar da kidayar jama’a data gidaje, to amma bayan watanni 17 shiru kake ji babu wani abu da aka yi, sannan kuma gwamnatin shugaba Bola Tinubu bata ce komai ba a kai ballantana sanar da ranar da za ayi kidayar.

Shirun da gwamnati mai ci yanzu ta yi wajen kin bayani a akan halin da ake ciki a game da batun kidayar shi ne ya janyo wannan zargi da jam’iyyar ta Labour ta yi.

Dr Yunusa Tanko, daya ne daga cikin masu magana da yawun jam’iyyar, kuma ya ce a yanzu dai shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinibu bashi da wani bayani da zai yi wa ‘yan Najeriyar kan yadda aka yi da kudaden kidiyar, saboda gazawar gwamnatinsa na sanar da ranar da za a gudanar da ita.

Ya ce “Abu ne mai kyau a gudanar da wannan kidaya domin ta haka ne za a san yawan ‘yan Najeriya dama irin abubuwan da ya kamata a yi musu, sannan kuma su wadannan kudade na gudanar da wannan kidaya tuni aka waresu, kuma har yanzu babu wani bayani a kan abin da ya hana yin kidayar, to abin tamabaya anan ina kudaden suke?”

Mai magana da yawun Peter Obin, ya ce ya kamata a fito fili a bayyanawa ‘yan Najeriya inda aka kwana a game da kidayar jama’a.

Dr Yunusa Tanko, ya ce,” Mun taso da wannan magana ne domin sanin halin da ake ciki, don yin shiru akan hakan ba dai-dai bane.”

Ya ce,” Hakkin duk wani dan Najeriya ne ya san halin da ake ciki a game da inda aka kwana a kidayar jama’a da aka shirya yi.”

A nata bangaren jam’iyya mai mulkin Najeriya APC, ta fito ta musanta dukkan zarge-zargen da jam’iyyar ta Labour ke mata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp