Gomman masu zanga-zanga sun yi dafifi a shelkwatar jam’iyyar PDP ta ƙasa da ke Abuja domin nuna rashin amincewa da kama aikin sabon sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sunday Ude-Okoye wanda kotun ɗaukaka ƙara ta ayyana a matsayin sakataren jam’iyyar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Bayanai sun nuna cewa shelkwatar jam’iyyar ta tafi hutun ƙarshen shekara ne a watan Disamba inda kuma a ranar Litinin ake sa ran komawa aiki ranar da sabon sakataren zai kama aiki.
To sai dai masu zanga-zanga da ke goyon bayan senator Sam Anyanwu wanda ake taƙaddama a kansa sun mamaye ƙofar ofishin inda suke ta ihun cewa ” ofishin sakataren jam’iyyar PDP na ƙasa akwai mai shi kuma senator Anyanwu ne sakataren.”
A baya-bayan nan ne dai kotun ɗaukaka ƙara ta Enugu ce ta ayyana cewa Sunday Ude-Okoye ne sakataren jam’iyyar halastacce.
An jibge jami’an tsaro a ƙofar shelkwatar jam’iyyar.