Home AFIRKA Tubabbun mayaƙan Boko Haram 124 za su koma rayuwar fararen hula a...

Tubabbun mayaƙan Boko Haram 124 za su koma rayuwar fararen hula a Nijar

Aƙalla tubabbun mayaƙan Boko Haram 124 ne mahukunta Jamhuriyyar Nijar suka yaye a ƙarshen makon da ya gabata, bayan da aka basu horo na musamman don sauya ɗabi’unsu da nufin ci gaba da rayuwar fararen hula a cikin jama’a.

A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne mahukuntan na Nijar suka gudanar da bikin yaye tubabbun mayaƙan na Boko Haram 124 adadin da ya ƙunshi har da ƙananan yara 44 bayan da aka basu horo kan ayyukan dogaro da kai daban-daban.

Gwamnan jihar Diffa da ke kudu maso gabashin ƙasar Janar Mahamadou Ibrahim Bagadoma yayin jawabinsa wajen bikin yaye tubabbun ƴan ta’addan ya ce abin farin ciki ne samun nasarar sauya ɗabi’un mutanen don mayar da su cikin fararen hula don ci gaba da rayuwa kamar kowa.

Wata sanarwa da ma’aikatar cikin gida ta fitar a Jamhuriyyar ta Nijar ta ce dukkanin tubabbun ƴan ta’addan 124 sun samu takardun shaidar kammala samun horo ta yadda ake da yaƙinin za su yi ingantacciyar rayuwa cikin fararen hula.

Wannan ne karon farko da Nijar ke yaye tubabbun mayaƙan Boko Haram tare da mayar da su cikin al’umma ko da ya ke hamɓararren shugaban ƙasar Bazoum Mohammed ya yi makamancin wannan yunƙurin a shekarar 2023 watanni gabanin yi masa juyin mulkin.

Tun shekarar 2017 ne tubabbun mayaƙan fiye da 700 suka ajje makamansu wanda ya bayar da damar fara yi musu horo na musamman don mayar da rayuwarsu da tunaninsu irin na sauran fararen hula.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp