Home General Bama Bukatar yin siyasa da Kwankwaso – APC kano

Bama Bukatar yin siyasa da Kwankwaso – APC kano

Jam’iyyar APC ta jihar Kano ta ce kokarin shigowa APC Kwankwaso yake yi shi ne Dalilin sa ya Abdulmumin Jibrin Kofa ya fara kiraye-kirayen a sami sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje.

“Maganar sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje da Kofa yazo da ita yaudara ce, a siyasance ba ma buƙatar yin siyasa tare da Kwankwaso”.

Mai magana da yawun Jam’iyyar APC reshen jihar Kano Ahmad S Aruwa ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da ya yayi da Hikima Radio dake Kano.

” So suke so dawo APC don su kwace ta daga wajenmu, domin Kwankwaso ya saba yin hakan tun da ya yiwa Malam Ibrahim Shekarau Wanda ta dole sai da muka bar masa APC muka koma PDP, haka kuma ya sake yi mana a PDPn don haka mun gano wayon”. Inji Kakakin APC

Ya ce idan da gaske ke gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ne ya kamata ya dai-data Kwankwaso da Ganduje, amma ba Kofa ba.

” Idan ka lura da yadda Kofa ya tsayyano mukaman da Kwankwaso ya rike da wadanda Ganduje ya rike zaka gane shi (Kofa) ya yi kankanta ya ce zai sulhunta Kwankwaso da Ganduje”. A cewar Aruwa

Kakakin APC reshen jihar Kano ya ce su ba sa bukatar yin sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje saboda a cewarsa daga karshe cewa za ayi a hade, kuma in an hade su za a cutar.

Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji Abdulmumin Jibrin Kofa a karshen makon da muke bankwana da shi , ya ce ya sama wajibi a sulhunta Ganduje da Kwankwaso saboda cigaban jihar Kano

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp