Home General ‘Najeriya za ta shiga ƙungiyar BRICS’

‘Najeriya za ta shiga ƙungiyar BRICS’

Gwamnatin Brazil ta sanar da cewa Najeriya ta amince ta shiga cikin ƙungiyar ƙasashen duniya da ake yi wa laƙabi da BRICS.

Brazil, wadda ita ce ke shugabantar ƙungiyar a 2025, a cikin wata sanarwa, ta bayyana cewa Najeriya “ta ƙasance ƙasa da ke ƙara ƙarfafa hulɗar dangantaka tsakanin ƙasashen ɓarin kudancin duniya da kuma sauya salon shugabanci”, wanda abu ne da Brazil ke bai wa muhimmanci.

“A matsayinta ta ƙasa ta shida mafi yawan al’umma a duniya, kuma mafi yawan al’umma a Afirka, kuma ɗaya daga cikin ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziƙi a Afirka, Najeriya na da kamanceceniyar manufofi da ƙasashen ƙungiyar,” kamar yadda sanarwar ta ma’aikatar harkokin waje ta Brazil ta sanar.

BRICS, ƙungiya ce ta ƙasashen da suka haɗa ba Brazil, Rasha, Indiya, China, Afirka ta kudu, Masar, Habasha, Indonesia, Iran da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Ana wa ƙungiyar kallon kini ta ƙungiyar ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziƙi ta duniya, wato G7.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp