Gwamnatin Tinubu za ta magance rashin aikin yi a Nijeriya – Ministan ƙwadago

Hoton Tinubu

Gwamnatin Nijerjiya tace za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen magance matsalar rashin aikin yi da ya ddabi alúmmar kasar.

Ministan ƙwadago na Najeriya, Muhammadu Dingyadi, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke kare kasafin kudin hukumar a gaban kwamitin majalisar dattija, karkashin sanatat Diket Plang, ministan ya tabbatar da yunkurin gwamnatin na magance matsalar ta rashin aiki yi.

“Muna aiki tuƙuru ba dare ba rana domin yaƙi da rashin aikin yi saboda yana cikin masu matuƙar muhimmanci a gare mu. Dukkan tsare-tsarenmu na koyar da sana’a mun yi su ne domin rage rashin aikin yi,” kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

A game da ƙididdigar rashin aikin yi na ƙasar, ministan bai bayyana adadi ba, inda ya ce, “muna ƙoƙari domin haɗa alƙaluma.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com