Home General Najeriya ta buƙaci a samar da ƙasashen Isra’ila da Falasɗinu masu cin...

Najeriya ta buƙaci a samar da ƙasashen Isra’ila da Falasɗinu masu cin gashin kansu

Najeriya ta yi kira da a samar da ƙasashen Isra’ila da Falasɗinu masu cin gashin kansu, inda ta ce hakan ne zai wanzar da zaman lafiya a yankin.

Ƙasar ta bayyana haka ne a lokacin da take maraba da tsagaita wuta da aka yi a Gaza tsakanin Isra’ila da Hamas.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Kimiebi Ebienfa ne ya bayyana haka a zantawarsa da tashar Channels mai zaman kanta a Najeriya.

“Najeriya na kira ga dukkan ɓangarori su haɗa kai domin tabbatar da an cimma sauran matakan yarjejeniyar tsagaita wutar, sannan Najeriya na kira da a samar da ƙasashen biyu na Isra’ila da Falasɗinu masu cin gashin kansu a matsayin hanya ɗaya tilo da za a tabbatar da zaman lafiya a yankin,” in ji Ebienfa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp