Home General Likitoci sun shiga yajin aiki a asibitocin Abuja

Likitoci sun shiga yajin aiki a asibitocin Abuja

Likitoci masu neman ƙwarewa sun shiga yajin aiki a Abuja, saboda rashin biyansu albashi da kuɗaɗen alawus da sauran buƙatunsu.

A wani taron manema labarai da ƙungiyar ta gudanar yau Laraba, a babban birnin Najeriyar, shugaban ƙungiyar, Dr George Ebong, ya ce yajin aikin na gargaɗi ne kuma kuma za su yi shi ne tsawon kwana uku.

Yajin aikin dai ya durƙusar da ayyuka a asibitocin gwamnati a birnin na tarayya.

Ebong ya ce sun shiga yajin aikin ne bayan ƙarewar wa’adin mako uku da suka ba gwamnati na gargaɗi.

Ƙungiyar ta koka da abin da ta ce wasarere da rashin kula da asibitoci da aka yi a Abuja.

Shugaban ya buƙaci ministan Abuja, Nyesome Wike da ya shiga lamarin don gujewa shiga yajin aikin sai-abin- da-hali ya yi.

A ranar Talata ne ƙungiyar likitoci ta yanke shawarar tsunduma yajin aikin bayan taron shugabanninta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp