Home General NLC Ta Buƙaci Ministan Makamashi Ya Sauka Daga Mukaminsa

NLC Ta Buƙaci Ministan Makamashi Ya Sauka Daga Mukaminsa

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC), ta yi kira ga Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu da ya sauka daga mukaminsa saboda yawaitar katsewar babban layin lantarki na ƙasa.

A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero ya fitar, ya ce ƙungiyar na takaicin yadda ɓangaren lantarkin Najeriya ya ƙi gyaruwa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A cewar Ajaero, “Idan har akwai ma’aikata ƙwararru waɗanda suka san makamar aiki a ma’aikatar makamashi, to lallai za’a iya kiyaye yawaitar abin kunyar nan da ake fuskanta na yawaitar katsewar layin lantarki a Najeriya. Magance matsalar ya kamata ministan ya yi, ba ya riƙa maganar cewa za su magance ta ba.

“Mun yi amannar cewa wannan ya nuna rashin ƙwarewa da gazawar ma’aikatar makamashin, wanda hakan ya sa muke mamakin me ya sa wanda ke jagorantar ma’aikatar ba zai sauka cikin mutunci ba”.

A karshe Ajaero ya kuma caccaki ministan bisa kasafta kashe naira biliyan 8 a kasafin kuɗin 2025 domin “wayar da kan ƴan Najeriya muhimmancin biyan kuɗin lantarki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp