Home General Likitoci sun shiga yajin aiki a asibitocin Abuja

Likitoci sun shiga yajin aiki a asibitocin Abuja

Likitoci masu neman ƙwarewa sun shiga yajin aiki a Abuja, saboda rashin biyansu albashi da kuɗaɗen alawus da sauran buƙatunsu.

A wani taron manema labarai da ƙungiyar ta gudanar yau Laraba, a babban birnin Najeriyar, shugaban ƙungiyar, Dr George Ebong, ya ce yajin aikin na gargaɗi ne kuma kuma za su yi shi ne tsawon kwana uku.

Yajin aikin dai ya durƙusar da ayyuka a asibitocin gwamnati a birnin na tarayya.

Ebong ya ce sun shiga yajin aikin ne bayan ƙarewar wa’adin mako uku da suka ba gwamnati na gargaɗi.

Ƙungiyar ta koka da abin da ta ce wasarere da rashin kula da asibitoci da aka yi a Abuja.

Shugaban ya buƙaci ministan Abuja, Nyesome Wike da ya shiga lamarin don gujewa shiga yajin aikin sai-abin- da-hali ya yi.

A ranar Talata ne ƙungiyar likitoci ta yanke shawarar tsunduma yajin aikin bayan taron shugabanninta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mazauna Kauye Sun yi Murna Yayin da Sojoji Suka Dakile Harin Ta'addanci, Sun Kwato Shanu a SakkwatoFarashin Canji da Yawa ya ja wa Najeriya Asara Fiye da Tallafin Man Fetur – CardosoGwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Kwamitin Bincike Kan Mutuwar Ma'aikatan Haƙar Ma'adinai 37 a Hukumar Kula da Haƙar Ma'adinai ta NSCDCMajalisar Dattawa ta 10 da Ma'anar Jagorancin Majalisa Daga Kabir AkintayoDarakta Janar na NITDA ya yi Kira da a Hada Hannu Kan Tsarin AI a Taron Manyan ShugabanniƳancin Sanin Gaskiya: Bayani Game da Tsarin Gudanar da Harkokin Sadarwa na Najeriya Daga Franklyn Ginger-EkeHOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa
X whatsapp