Home General Mun Samu Kasuwancin Magunguna na Kano a Rikice- Kwamishinan Lafiya

Mun Samu Kasuwancin Magunguna na Kano a Rikice- Kwamishinan Lafiya

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta Sami kasuwancin magunguna na jihar, bayan ƙarewar shekaru takwas na zangon mulki na biyu na Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, a cikin yanayi mara daɗi.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana haka yayin da yake karɓar shugabannin Кungiyar Masu Haɗa Magunguna da Sarrafa su ta Najeriya, reshen jihar Kano, da suka ziyarci shi a ofishinsa.

Ya kara da cewa sun samu kasuwar magani, musamman Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Asibiti (DMCSA), hukuma ɗaya tilo da gwamnati ta amince ta samar wa asibitoci magunguna masu inganci da sauƙi, a durƙushe tana buƙatar ɗauki.

Dakta Labaran ya yi farin ciki da samun dunƙulalliyar kasuwar hada-hadar magunguna a Ɗangwauro kasancewar abubuwa sun fara dawowa daidai, ya ƙara da cewa abin da kawai ya rage shi ne tilasta amfani da kasuwar yadda ya kamata domin a tsaftace kasuwancin magunguna a jihar.

Kwamishinan ya ce sirrin da ke tattare da samun nasarar ayyukan samar da magunguna a Kano ta biyo bayan neman shawarar ƙwararru kan harkokin magunguna da yake yi game da duk wani abu da ya shafi harkar kafin ya tura wa Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ya bayyana cewa, gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf tana yin ayyukan da take yi ne domin al’umma, yana mai shawartar masu kasuwancin magani da su yi taka-tsantsan da jin tsoron Allah yayin da suke gudanar da ayyukansu, domin za a iya sake canja tare da sarrafa maganin da wa’adinsa ya ƙare a sake mayar da su kasuwa, yana mai yarda da cewa mutum mai tsoron Allah bai zai yi irin wannan ƙazamin kasuwancin ba.

Dakta Labaran ya ce ya yi farin ciki sosai da ɗaukar nauyin ɗalibai zuwa ƙasar Indiya su yi karatun haɗa magunguna da sarrafa su a lokacin da yake kwamishina a tsakanin shekarar 2011 da 2015, ya ce a lokacin ‘yan Kano masu rajista a wannan ilimin 51 ne kawai, wanda hakan ya sa Gwamna Kwankwaso ya umarce shi ya tantance mutum 100 aka tura su Indiya, da mafi yawansu yanzu haka suna hidimta wa Kano.

Da yake jawabi tun da fari, Shugaban Кungiyar, Famasis Mustafa Umar ya ce sun zo ma’aikatar ne domin su nuna goyon bayansu ga ƙoƙarin kwamishinan na kawo sauyi a sashin lafiya na jihar nan.

Ya nuna farin cikinsa da cewa dawowar kwamishina ta zo a lokacin da ya dace saboda masu ilimin haɗa magunguna da sarrafa su na jihar Kano suna cikin damuwa mai tsanani game da makomar DMCSA, amma yanzu sun samu nutsuwa saboda abubuwa sun fara dawowa daidai da ta kai yanzu ake samun magani kashi 96 cikin 100 a asibitoci idan an kwatanta da baya da ake samun kaso 30 kawai.

Shugaban ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa naɗa ɗaya daga cikinsu, Famasis Aminu Bashir a matsayin Babban Sakatare, wanda shi ne irinsa na farko a tarihin jihar Kano, yana mai tabbatar da cewa babban sakataren zai yi aiki tuƙuru wajen ci gaban aikin gwamnati duba da ƙwazo da jajircewarsa a aiki.

Daga nan sai ya sanar da kwamishinan cewa a watan Nuwamba, na wannan shekarar, jihar Kano za ta karɓi baƙuncin taron Кungiyar Masu Samar da Magunguna da Sarrafa su da ake sa ran ‘ya’yan ƙungiyar dubu uku zuwa dubu biyar za su ziyarci Kano, inda ya nemi gudummawar gwamnati.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp