Home General Ƙara kuɗin kira da na data rashin adalci ne- NLC

Ƙara kuɗin kira da na data rashin adalci ne- NLC

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya ta yi kira ga ƴan Najeriya su fara shirye-shiryen dakatar da amfani da kamfanoninin sadarwa domin nuna adawarsu ga amincewa da ƙarin kashi 50 na kuɗin kira da data da gwamnatin tarayya ta yi.

A wata sanarwa da NLC ta fitar a jiya Laraba, ta ce ƙarin kuɗin rashin adalci ne ga ƴan ƙasar, waɗanda a yanzu haka suke fuskantar ƙalubale saboda matsin tattalin arziki.

Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana damuwarsa kan ƙarin, inda ya ce, “wannan matakin, wanda ya zo a daidai lokacin da ma’aikata da sauran ƴan ƙasa suke fama da matsin tattalin arziki, tamkar ba kamfanonin sadarwar wuƙa da nama su yi yadda suke su da ƴan ƙasar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

“Harkokin sadarwa na cikin abubuwa masu muhimmanci domin sadarwa da neman labarai. Kuma ko a yanzu ma ƙaramin ma’aikacin Najeriya yakan kashe kusan kashi 10 na albashinsa wajen sayan katin waya da data. Misali ma’aikacin da ke karɓar albashin naira 70,000, idan yana kashe naira 7,000 ne, yanzu zai fara kashe kusan naira 10,500 ne a waya.”

Ya kuma caccaki gwamnatin bisa yadda ta amince da ƙarin cikin gaggawa, amma ta ɗauki dogon lokaci kafin ta amince da mafi ƙarancin albashi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
COAS Ya Bukaci Bojojin Nijeriya da su Mayar da Hankali Wajen Kare Rayukan Fararen HulaTURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci MatsalolintaDangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige Fubara
X whatsapp