Home General NAPTIP ta ceto mata 9 masu juna biyu da aka kulle a...

NAPTIP ta ceto mata 9 masu juna biyu da aka kulle a masana’antar jarirai

Hukumar dake yaƙi da safarar mutane ta Najeriya NAPTIP ta bayyana cewa ta samu nasarar ceto wasu mata guda 9 masu juna biyu a wani gidan da ake ajiye  matan domin su riƙa haihuwar yaran da ake sayarwa.

Jami’in yaɗa labarun hukumar ta NAPTIP Vincent Adekoye ne ya bayyana nasara da jami’ansu suka samu ga manema labaru a yayin da yake gabatar musu da jawabi.

Adekoye ya ƙara da cewa an sami wurin ne a cikin wani rukunin gidaje a yankin Ushafa dake ƙaramar hukumar Bwari dake Abuja babban birnin tarayyar ƙasar, a yayin da ya ke cewa sun mamayi wannan wuri ne bayan wasu bayanai da suka samu daga wasu masu kishin ƙasa.

Ya ce an samu waɗannan mutane ne a kulle a cikin wani gida a sanadiyar ɗaya daga cikin waɗanda suka killace matan da ba’a fayyace shi ba, bayan da aka ɗaukesu aikin na aika-aikar da suka nema ta  wani shafinsu na yanar gizo.

Adekoye ya kuma ce, Darakta-Janar ta Hukumar, Hajiya Binta Adamu-Bello, ta yabawa bangaren shari’a, bisa gagarumin hukuncin da aka yanke na yankewa wani Bishop Kenneth Duke hukunci.

An dai ce Duke ya yi wa wata yarinya ‘yar shekara 12 fyade, wacce diya ce ta ɗaya daga cikin mabiya cocinsa a Abuja.

Shugabar ta ce wannan hukuncin na iya zama izna ga ire-iren masu irin wannan aika-aikar, yayin da ta yi gargadin cewa hukumar ba za ta kyale duk wanda ya karya dokarta ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp