Home General Bello Turji ya bayyana aniyar mika wuya – Manjo janar Christopher Musa

Bello Turji ya bayyana aniyar mika wuya – Manjo janar Christopher Musa

Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Janar Christopher Musa a jiya Juma’a ya bayyana cewa fitaccen shugaban ‘yan ta’adda Bello Turji ya bayyana aniyar mika wuya. Ya bayyana hakan ne a lokacin da aka gayyace shi a cikinn wani shiri na gidan talabijen mai zaman kan sa a kasar.

Manjo Janar Christopher Musa, ya kara da cewa hare-haren da sojoji suka yi a baya-bayan nan, wanda ya kawar da wasu kwamandojin Turji da wasu mukarrabansa, ya karya logon shugaban ‘yan ta’addan.

Hakan ne ya tilasta masa sakin da dama daga cikin mutanen da ya yi  garkuwa da su, lamarin da ke nuni da shirinsa na ajiye makamai.

Yan ta’adda suna cikin al’umma; mutane sun san su. Don haka, wani lokacin idan sun gan su, kafin ka sami bayanin, kamar sa’o’i biyu ne – mutumin ya motsa. Don haka idan bayanin ya same ka, kafin ka matsa ya bar yankin.” Inji Janar Musa.

Ya kara da cewa, “Amma zan iya gaya muku, mun fitar da na biyu a matsayinsa, mun fitar da mafi yawan hakimansa, hasali ma ya tilastawa yanzu ya saki mafi yawan mutanen da ke karkashinsa.

Ina gaya muku kwanan nan ya fara cewa ba ya son komai, a shirye yake ya mika wuya.” Duk da cewa Turji ya bayyana aniyar mika wuya, Janar Musa ya jaddada muhimmancin daure masu aikata ta’addanci, musamman wadanda ke da alhakin mutuwar ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp