Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga rundunar ƴansandan Najeriya su dinga amfani da ƙwarewa, da kaucewa bayanan da ka iya tada hankali yayin gudanar da ayyukansu, musamman a jihar.h
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Hakan na zuwa ne bayan damuwar da aka nuna kan sanarwar ‘yan sandan jihar Kano na yiwuwar za a kai harin ta’addanci a jajibaren bikin Mauludin da mabiya ɗarikar Tijjaniyya suke gudanarwa a duk shekara, da aka shirya yi a filin wasa na Sani Abacha da ke jihar.
Kwankwaso ya bayyana hakan a shafinsa na X, inda ya ƙara da taya mabiya ɗarikar Tijjaniyya da gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da Sarki Sanusi Lamido Sanusi II, kan nasarar yin taron Maulidin lami lafiya.
A makon da ya wuce ne dai, rundunar ‘yansandan jihar Kano ta fitar da sanarwar gargaɗi kan barazanar kai harin ta’addanci a jihar, da buƙatar a dakatar da bikin Maulidin da yake tara ɗaruruwan mutane daga sassan jihar da jihohi makofta.











