Majalisar dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar ta dauki matakai kan Kangwaye dake jihar

Majalisar jihar Kano
Majalisar jihar Kano

Majalisar dokokin jihar Kano dake arewa maso yammacin Nijeriya ta bukaci gwamnatin jihar da ta umarci masu kangwaye (filayen da ba’a gina ba ko tsofaffin gidajen da ba kowa a ciki) dasu gine ko kuma su sayar da su.

Wannan na zuwa ne bayan kudurin da Dan majalisa mai wakiltar Karamar hukumar Kiru Usman Abubakar Tasiu ya gabatarwa zauren majalisar.

Kiru ya ce yawancin kangwaye da gidajen da baa karasa ba a jihar sun zama wuraren lalata tarbiya da barazanar tsaro.

Da yake bada gudunmuwa akan kudurin dan majalisa mai wakiltar Karamar hukumar Madobi Sulaiman Mukhtar Ishaq ya ce ba iya kangwaye ba, hatta gidajen da aka gina na kwankwasiya da Amana city da Bandirawo sun zama barazanar tsaro da tarbiyyar al’ummar Kano.

Majalisar ta kafa kwamiti domin binciko mata lamuran kangwaye, inda zata mika shi ga gwamnatin Kano domin tabbatar da gyara a al’amarin.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com