Home General Sojoji Nijeriya na cigaba da farautar Bello Turji

Sojoji Nijeriya na cigaba da farautar Bello Turji

Dakarun Operation Fansan Yamma tare da haɗin gwiwar jami’an tsaron farin kaya (DSS), sun ce sun ƙwace tarin makamai a karamar hukumar Kauran Namoda na jihar Zamfara.

Dakarun sun kai samamen ne bayan samun bayanan sirri kan masu safarar makamai daga Jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya.

Wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran rundunar Laftanar-Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce sun kaddamar da farmaki ranar 27 ga watan Janairun 2025, abin da ya kai ga ƙwato makaman kan hanyar Namoda zuwa Zurmi.

Ya ce waɗanda ake zargin sun tsere zuwa cikin daji tare da barin motarsu bayan artabu da sojoji.

Kanal Abubakar ya ce bayan bincike da suka yi a cikin motar, sun gano makamai da dama da suka haɗa da bindigar AK-47 guda tara da harsasai daban-daban.

A ɗaya gefen, dakarun sun ce suna cigaba da neman inda Bello Turji yake wanda ake nema ruwa a-jallo – wanda yake cigaba da tserewa sojoji ta hanyar guduwa daga maɓoya zuwa maɓoya.

Dakarun sun tabbatar da cewa suna aiki tukuru domin kama Turji domin mayar da zaman lafiya a al’ummomin da suka addaba da hare-hare.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp