Home General NLC za ta yi zanga-zanga don adawa da ƙarin kuɗin kiran waya

NLC za ta yi zanga-zanga don adawa da ƙarin kuɗin kiran waya

Ƙungiyar ƙwadago ta NLC a Najeriya ta ce za ta gudanar da gagarumar zanga-zanga ranar Talata 4 ga watan Febrairun 2025, domin adawa da ƙarin kuɗin kiran waya da kashi 50 wanda Hukumar Sadarwa ta Najeriya NCC ta amince da shi.

Wata sanarwa da ƙungiyar ta hannun shugabanta Joe Ajaero, ya ce sun ɗauki matakin ne a wani taron gaggawa da suka gudanar ranar Laraba.

NLC ta ce zanga-zangar za ta zama gargaɗi ga hukumomi kan yunkurin kakabawa mutane ƙarin kuɗin kiran waya a ƙasa kuma da albashi mafi ƙanƙanta bai wuce naira 70,000 ba, ga kuma ƙarin farashin mai da na abinci da lantarki da kuma ƙaruwar hauhawarar farashi.

Ƙungiyar ta buƙaci rassanta na jihohi da su fara shirya mambobinsu domin shiga zanga-zangar ta ƙasa baki-ɗaya, inda ya yi kira ga ƙungiyoyin fararen hula da su ma su fito.

Ta kuma yi kira ga ma’aikata da kuma ɗaukacin ƴan Najeriya da su tsaya kai da fata wajen yin watsi da wannan tsari da kuma waɗanda ba su alheri gare su.

Ƙungiyar ƙwadagon ta kira yi gwamnatin tarayya da NCC da hukumar majalisar tarayya da su zauna don tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin sake duba wannan ƙari a daidai lokacin da ƴan ƙasar ke fama da matsin tattalin arziki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp