Home General Gwamnatin Kano za ta fito da wasu hanyoyin tattara zakkah

Gwamnatin Kano za ta fito da wasu hanyoyin tattara zakkah

Gwamnatin Kano ta ce za ta fito da wasu da Sabbin hanyoyin tattara zakkah tare Kuma da rabawa mabukata yadda yakamata

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka Lokacin kaddamar da shugabannin hukumomi biyu na Shari’a da na Zakkah a gidan Gwamnati.

Abba Kabir Yusuf ya ce Jihar Kano na da dimbin attajirai, to sai dai a bangare guda ta na fama da yawan almajirai da mabarata , Wanda ya bukaci hukumar Zakkah da KHubsi da ta fito da wasu hanyoyi na karba Zakkah daga wajen attajirai a wani yunkuri na rage yawan mabarata a JIhar kano.

Shugabannin hukumomin da Gwamnan ya kaddamar sun hada da Barrister Habibu Shekh Dan Almajiri a matsayin Shugaban hukumar Zakkah da Khubsi, sai Shekh Abbas Abubakar Daneji a matsayin Shugaban hukumar Shari’a.

Sauran wakilan hukumar sun hada da Shekh Malam Ali Dan Abba a matsayin kwamishina na biyu a hukumar shari’ah da Malam Abubakar madatai Mai Ashafa da sayyadi Nafi’u Umar Harazumi da Kuma alaramma Gwani Hadi Gwani Tahir

Wakilinmu na fadar Gwamnati ya ruwaito mana Gwamnan na Jan hankulan malaman da su yi amfani da gogewa da Ilimi wajen fito da Sabbin tsare tsare da za su kawo ci gaban addinin musulunci a Jihar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp