Dakarun Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 82 tare da kama 198 a mako guda

Shelkwatar tsaron Najeriya ta ce dakarunta sun kashe ƴan ta’adda 82  tare da kama guda 198, suka kuma ceto mutane 93 da aka yi garkuwa da su a cikin mako guda da ya wuce a sassan ƙasar.

Daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar, Manjo Janar Markus Kangye,  ne ya bayyana haka a Abuja,  a yayin da ya ke yi wa manema labarai bitar nasarorin  da dakarun ƙasar suka samu.

Kangye  yace dakarun sun kuma ƙwace ɗimbim makamai da ababen hawa a daga ƴan ta’addan a samamen da suka yi daga ranar 14 zuwa 21 ga watan Fabrairu.

Ya ce dakarun sun ƙwace bindigogi da suka haɗa da AK47 guda 46, bindigogin da aka ƙera a gida guda 18, sai bindigogin zari-ruga guda 19 da harshasai sama 1,200.

Kakakin ma’aikatar tsaron ya ƙara da cewa ƴan ta’addda 41 sun miƙa wuya ga dakarun rundunar Operation HADIN KAI a yankin arewa maso gabashin ƙasar, kuma daga cikin su akwai manya baligai 41, sai yara 19.

Janar Kangye ya ƙara da cewa dakarun na Najeriya sun kama masu satar mai a yankin Kudu maso Kudancin ƙasar, sun kuma daƙile satar da kiyasta darajarta ta kai naira 587.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com