Gwamnatin Kano na shirin kafa kwamitin bincike kan kungiyoyin masu zaman kansu NGOs

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da shirin gudanar da bincike mai zurfi kan ayyukan ƙungiyoyi masu zaman kansu (NGOs) a jihar, domin tabbatar da cewa sun yi daidai da al’adun Musulunci da kuma ka’idojin zamantakewar al’umma.

Matakin ya zo ne bayan bayyanar wata ƙungiya da ake zargi da yada ra’ayin auren jinsi, abin da ya haifar da cece-kuce a cikin jihar.

Gwamnatin ta ce za a tantance ayyukan waɗannan ƙungiyoyi, musamman ta hanyar duba tushen samun kuɗinsu, da shugabanninsu, da kuma bin dokokin ƙasa.

A cikin wannan tsari, za a yi amfani da ka’idojin ƙasa da na duniya kamar dokokin FATF (wanda ke yaƙi da satar kuɗi), da dokokin Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, da kuma Dokar Kamfanoni ta Najeriya (CAMA 2020) don tabbatar da gaskiyar ayyukan ƙungiyoyin.

Gwamnati ta bayyana cewa manufar ita ce kare al’adun gargajiya na al’umma, da ƙarfafa gaskiya, da kuma hana amfani da kuɗin kasashen waje don ayyukan da suka shafi tsaro.

Matakin ya zo ne tare da naɗin kwamishinan ma’aikatar yaɗa labarai ta jihar Kano Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zaba a matsayin wanda zai jagoranci aiwatar da wannan binciken.

Sai dai wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu sun nuna adawa da wannan yunkuri, inda gwamnati ta yi zargin cewa masu adawar na tsoron bayyana “manufofinsu na ɓoye” da suka saba wa al’adun jihar Kano.

Gwamnati ta ce ƙungiyoyin da ke aiki bisa doka ba za su ji tsoron wannan bincike ba, yayin da binciken zai ƙara ƙarfafa amincewar jama’a da su.

Gwamnatin ta bayyana cewa ƙin yarda da wannan tsari na iya nuna wata manufa ta ɓatanci da rashin gaskiya, kamar satar kuɗi ko karya ka’idoji.

Dr. Abraman Sunday, shine shugaban ƙungiyar fararen hula ta Integrity Group, ya yaba wa matakin, yana mai cewa zai inganta aikin ƙungiyoyi masu zaman kansu.

Ana sa ran za a fara aiwatar da wannan tsari cikin ‘yan makonnin nan.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1486 days 5 hours 7 minutes 1 second,

Baptist School Students, Kaduna
1468 days 6 hours 48 minutes 26 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com