Najeriya da China sun rattaba hannu akan yarjejeniyar samar da makamashi mara gurɓata muhalli da ya kai Yuro biliyan 7 da miliyan ɗari 6 da zummar sauyawa daga amfani da makamashi mai gurɓata muhalli daidai da yadda dokokin duniya suka tanada.
A ƙarshen makon da ya gabata ne aka tabbatar da wannan yarjejeniya a hukumance a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom a tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanin APPL Hydrogen Limited (AHL), da LONGi Green Energy Technology Company Limited na ƙasar China.
Read Also:
Za a gudanar da wannan aiki ne yankin da aka sakar wa yan kasuwa mara su gudanar da sabgoginsu, wato Liberty Free Trade Zone da ke garin Atabrikang a ƙaraamar hukumar Ibeno ta jihar Akwa Ibom.
Kamfanin LONGi, wanda ke kan gaba a hakar sauyawa zuwa amfani da makamashi mara gurɓata muhalli a duniya, da AHL na Najeriya, wanda ya ƙware wajen samar da makamashi da ba ya illata muhalli ne za su yi haɗaka don tafiyar da aikin, kamar yadda yake a cikin yarjejeniyar fahimtar juna da aka yi.
Da yake jawabi a yayin rattaba hannu a yarjejeniyar, ministan kimiyya da fasaha na Najeriya, Uche Nnaji ya jaddada mahimmancin shirin a koƙarin da Najeriya ke yi wajen sauyawa zuwa amgfani da makamashin da ba ya illa ga muhalli.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1485 days 19 hours 13 minutes 17 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1467 days 20 hours 54 minutes 42 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com