Tinubu ya bawa Jega Mukami

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya nada Farfesa Attahiru Jega a matsayin mai ba shi shawara kuma babban jami’in kwamitin bunkasa kiwon dabbobi na kasar.

Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.

Attahiru Jega mai shekaru 68 ya rike mukamin shugaban hukumar zaben Nijeriya daga shekarar 2010 zuwa 2015.

Kafin mukamin da Shugaba Tinubu ya ba shi a yammacin Jumma’ar nan, shi ne ya jagoranci kwamitin gyaran kiwon dabbobi da ya bai wa gwamnatin Tinubu shawarar kafa ma’aikata ta musamman don bunkasa kiwon dabbobi wacce yanzu ke da minista.

Sanarwar ta ce ana sa rana Farfesa Attahiru Jega zai yi amfani da gogewar da wajen habbaka harkokin kiwon dabbobi a Nigeria kamar yadda suka bayar da samar da ma’aikata sukutum da guda.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1487 days 4 hours 43 minutes 50 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1469 days 6 hours 25 minutes 15 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com