Hukumar Kula da Albarkatun Mai Na Ƙasa (NMDPRA) ta bayar da lasisin buɗe sabbin matatun man fetur a Najeriya.
Hukumar ta ce ta ba wasu kamfanoni guda uku lasisin ne domin buɗe matatun a jihohin Abia da Delta da Edo.
Read Also:
Shafin intanet na tashar Channels ne ya kalato labarin daga shafin X na NMDPRA, inda ya ƙara da cewa za a buɗe Matatar Eghudu wadda za ta iya tace ganga 100,000 a kullum a jihar Edo.
Za kuma da Matatar MB wadda za ta riƙa tace ganga 30,000 a kullum a jihar Delta, sai Matatar HIS wadda ita kuma za ta riƙa tace ganga 10,000 a kullum a jihar Abia, kamar yadda sanarwar, wadda shugaban hukumar, Farouk Ahmed ya bayyana ta nuna.
Idan aka kammala su, matatun guda uku za su riƙa tace ganga 140,000 ke nan a kullum.