Babbar jam’iyyar a Najeriya wato PDP ta sake ɗage babban taronta na ƙasa wato taron NEC, wanda yanzu aka mayar ranar 15 ga Mayun 2025.
Jam’iyyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, wadda babban sakatarenta, Sunday Ude-Okoye ya sanya wa hannu.
Asali jam’iyyar ta sanar za ta yi babban taron ne a ranar 13 ga Maris, sannan aka ɗage saboda wasu zaɓukan cike gurbi da aka yi a wasu jihohi da yankuna.
Tun a shekarar da ta gabata ce dai aka saka ranar babban taron na 98, amma ana ɗagewa, wanda wataƙila hakan bai rasa nasaba da wasu matsaloli da jam’iyyar ke fuskanta.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1486 days 15 hours 42 minutes 29 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1468 days 17 hours 23 minutes 54 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com