Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce bai bar jam’iyya mai mulki ta APC ba har sai da tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya amince da batun barinsa jam’iyyar APC da komawa jam’iyyar SDP.
“Da saninsa na bar APC. Sai da na je ranar Juma’a na faɗa masa cewa zan bar jam’iyyar. Saboda babu wani abun da nake yi ba tare da na sanar da shi ba.
Sashen Hausa na bbc ya wallafa El-Rufai na cewa “Ko lokacin da nake gwamnan Kaduna da zan naɗa kwamishoni sai da na kai masa jerin sunayen domin ya duba ya gani ko a ciki akwai wanda ya taɓa zagin sa”.
Bayan ya duba ya ce ba matsala Allah ya yi albarka. Duk abin da zan yi sai na yi shawara da shi.” In ji Malam El-Rufai.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1485 days 14 hours 41 minutes 57 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1467 days 16 hours 23 minutes 22 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com