Majalisar wakilan Nijeriya ta ce a yau zata fara tsefe rahoton kwamitin sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin dokar haraji.
Kakakin Majalisar, Hon. Tajudeen Abbas ne ya bayyana haka a zaman majalisar na ranar Laraba.
Hon Tajudeen ya ce majalisar za ta ɗauki tsawon wunin yau, Alhamis tana nazari da muhawara kan sassan ƙudirin dokar daban-daban.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Kakakin majalisar ya kuma yi kira ga duka mambobin majalisar su halarci zaman domin bayar da tasu gundunmawa kan rahoton kwamitin sauraron ra’ayin jama’ar.
Tuni dai kwamitin sauraron ra’ayin jama’ar – ƙarƙashin jagorancin shugaban kwamitin kuɗi na majalisar, Hon James Abiodun Faleke – ya kammala sauraron jin ra’ayin jama’a inda ya miƙa rahoton nasa a gaban majalisar a ranar Talata
A watan Oktoban bara ne shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya gabatar da ƙudurori huɗu da suka shafi haraji a gaban majalisun dokokin ƙasar, domin amincewa da su.











