Home General Inganta rayuwar AL’umma ce a gabana ba zaben 2027

Inganta rayuwar AL’umma ce a gabana ba zaben 2027

Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ya mayar da hankali ne ga kyautata rayuwar ƴan ƙasar, amma ba wai ga zaɓen 2027 ba.

Mai taimaka wa shugaban kan harkokin sadarwa, Sunday Dare wanda ya bayyana haka a shafin X ranar Juma’a, ya ce za a ga nasarorin da gwamnatin Tinubu ta cimma zuwa karshen wa’adinsa na mulki, ta yadda ya kawo ci gaba ga ɓangaren tattali arzikin ƙasar.

Sanarwar ta Mista Dare na zuwa ne a daidai lokacin da turka-turkar siyasa da kuma tsadar rayuwa ke ƙaruwa a ƙasar.

“Tinubu bai damu da babban zaɓen Najeriya na gaba ba. Ya damu ne kawai kan irin ci gaban da zai kawowa ƴan Najeriya,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa shugaban ya kuma damu kan yadda tsare-tsaren da ya kawo za su haifar da ɗa mai ido.

“Mun ga saukar hauhawar farashi, mun ga kyautatuwar hada-hadar kasuwanni da kuma harkokin shige da fice na kayayyaki,” in ji sanarwar.

Ta kuma ce an samu zuba-jari da ya kai naira biliyan 50, har ma da saukar farashin kayayyaki.

Sai dai ƴan Najeriya na ci gaba da ƙoƙawa dangane da tsadar rayuwa da suka ce manufofin shugaban sun jefa su, musamman ma cire tallafin man fetur da ya yi lokacin rantsuwar kama aiki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp