Home General Tinubu ya bayyana Vice Admiral Ibas matsayin Gwamnan Jihar Rivers na riko

Tinubu ya bayyana Vice Admiral Ibas matsayin Gwamnan Jihar Rivers na riko

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tunubu Ya sanya Dokar Ta baci a jihar Ribas sakamakon Rikici da yaki ci yaki cinyewa.

Bola ahmad Tunubu wanda yayi wani gajeren jawabi da Yammacin wanann rana a fadar Shugaban kasa, Yace abinda ke faruwa a jihar Ribas ba zai yiwu su bari ya cigaba da faruwa ba.

Saboda an gaza samun daidaito tsakanin gwamnan jihar Fubara da Majalisar Dokokin jihar tun bayan da kotun Koli ta yanke Hukunci.

Bola ahmad Tunubu ya kara da cewa Gwamnan jihar ya dauki matakin rushe Zauren majalisar kuma ya gaza gyarawa, wanda hakan yasa Yan majalisar Jihar suka gaza samun cikakken matsuguni da zasuyi aikinsu kamar yadda kundin tsarin Mulkin kasar nan ya tanadar.

Shugaban kasa bola Ahmad Tunubu ya sanar da Vice admiral Ibokette Ibas Mai ritaya a matsayin wanda zai kula da Tafiyar da jihar Ta Ribas

Tinubu yace ya samu rahotanni dake nuna Yadda Yan bindiga suka fara kai hare hare manyan bututun Manfetur wanda hakan barazana ne.

Kuma Gwamnan jihar Da Mataimakinsa basu zo sun sanar dani yanayin tsaro dake fuskantar Jihar ba, don haka a matsayina na Shugaban kasa wajibi nayi amfani da dokar kasa da ta bani dama wajen kare rayuka da dukiyoyin alumma wajen sanya dokar tabaci a jihar.

Ina sanar da Yan Nijeriya cewa daga yau na dakatar da Gwamnan jihar ribas da Mataimakinsa da kuma dukkan Yan Majalisar jihar har na tsawon watanni 6.

Shugaban kasa bola Ahmad Tunubu ya sanar da Vice admiral Ibokette Ibas Mai ritaya a matsayin wanda zai kula da Tafiyar da jihar Ta Ribas

Sai dai kuma bangaren Sharia na jihar zai cigaba da tafiyar da aikinsa kamar Yadda suka saba acewar Shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp