Kamfanin matatar mai ta Dangote ta sanar da cewa ta dakatar da sayar da man fetir da kuɗin Najeriya wato Naira.
Kamfanin ya faɗi hakan ne a wata sanarwa da ya aike wa dilallan man fetir a yau Laraba.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sanarwar ta ce ”Kamfanin tatar mai ta Dangote ta dakatar da sayar da fetir a naira na wani lokaci. Hakan ya zama wajibi ne saboda kaucewa rashin daidaito da ake samu tsakanin ribarmu da kuɗin da muke sanya wa masu sayen ɗanyan mai wanda a yanzu galibi da dala muke yi.”
Kamfanin ya kuma ƙara da cewa bisa wannan dalilin, wajibi ne su sauya kuɗin da suke siyar da man domin ya yi dai-dai da kuɗin da su ke siyan ɗanyen mai na wani ɗan lokaci.
Sanarwar ta kuma ce kamfanin ya dukufa wajen biyan buƙatun kasuwannin Najeriya, kuma da zarar sun karɓi jiragen dakon mai da aka siya da Naira daga kamfanin NNPC, za su ci gaba da siyar da man fetir ɗin da Naira.











